Saudiyya ta yi Allah-wadai da kisan da aka kai wa manoma a Najeriya

Saudiyya ta yi Allah-wadai da kisan da ake zargin mayakan Boko Haram sun yi wa wasu manoman shinkafa a garin Koshebe da ke jihar Borno a arewa maso gashin Najeriya.
Cikin wani saƙon da tawallafa a shafinta na Twitter, ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya ta ce abin takaici ne yadda mahara ke kai wa fararen hula hare-hare waɗanda ba su ji ba basu gani ba.
Ta ce kuma “Muna isar da ta’aziyyarmu ga iyalan waɗanda aka kashe da da gwamnati da kuma ɗaukacin al’ummar Najeriya.
Bahrain ma ta miƙa irin wannan ta’aziyya ga Najeriya tana mai fatan ganin an kawo ƙarshen irin waɗannan hare-hare a kusa.