Ƙananan hukumomin da za su bai wa ɗan takara nasara a zaben jihar ondo

Ƙananan hukumomin da za su bai wa ɗan takara nasara.

Ƙananan hukumomin da za su bai wa ɗan takara nasara.

Ondo

Yayin da masu zaɓe ke kammala kaɗa ƙuri’arsu a zaɓen gwamnan Jihar Ondo, INEC ta ce mutum 1,822,346 ne ke da rajistar kaɗa ƙuri’a daga ƙaramar hukuma 18 – kodayake dai ba duka ne za su yi zaɓen ba.

Ƙananan hukumomin su ne: Akoko North East, Akoko North West, Akoko South East, Akoko South West, Akure North, Akure South, Ifedore, Ile Oluji/Okeigbo, Ondo East, Ondo West, Owo, Ilaje, Okitipupa, Ose, Odigbo, Ese Odo, Idanre da Irele.

Sai dai, ƙaramar hukuma uku ne kawai ke da ƙarfin faɗa-a-ji idan ana maganar sakamakon da zai bai wa ɗan takara nasara.

Akure Ta Kudu

Akure Ta Kudu ce ƙaramar hukuma mafi girma a Ondo, inda take da yawan jama’a fiye da mutum 480,000 da kuma masu katin jefa ƙuri’a fiye da 280,000.

Ondo Ta Yamma

Ita ce ƙaramar hukuma ta uku a yawa, inda take da yawan masu kaɗa ƙuri’a sama da 150,000.

Ƙaramar Hukumar Owo

Gwamna Rotimi Akeredolu ya fito ne daga Owo kuma shi ne ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen na 2020.

Owo na da yawan masu katin zaɓe fiye da 119,000. Ana ganin mazauna yankin za su zaɓi ɗansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here