Ƙananan Hukumomi 34 na jihar Katsina, ne zasu Amfana da Tallafin Azumi na Gwagwaren Katsina Dikko Umaru Raɗɗa
A ci gaba da rabon kayayyakin masarufi da Gwagware Foundation ƙarƙashin (Cibiyar tallafawa marayu da gajiyayyu ta Dakta Dikko Umaru Radda) Karkashin jagorancin Shugaban Cibiyar, Alhaji Kabir Usman Amoga.
A ranar Lahadi 3 ga watan Fabrairu, da yayi daidai da 2 ga Watan Ramadana, an kaddamar da rabon Shinkafa, Gero, Taliya da sauran kayayyakin abinci a ofishin Cibiyar ta Gwagware dake daura da ofishin, KATARDA, dake kan titin kano a cikin garin Katsina, inda manyan baki suka hallara domin ƙaddamarwa da kuma sheda rabon bisa tsari kamar yanda aka tsara.
Daga cikin bakin da suka halarci wajen rabon kayan abincin akwai Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar katsina Rt Hon Ya’u Umar gwajogwajo, mai bawa Gwamnan Katsina shawara akan Siyasa, Hon. Kabir Sha’aibu Charanci, Kwamishinan Ilimi na jihar katsina Farfesa Badamasi Lawal, Dan Majalisar karamar hukumar Charanci Hon. Isa kuraye, Hajiya Binta Dangani, Dantakarar Majalisar tarayya daga karamar hukumar Katsina, Alhaji Musa Gafai.
Da yake jawabi a wajen Ƙaddamarwa, Dantakarar Gwamnan jihar Katsina kuma shugaban hukumar kanana da matsakaitan masana’antu ta Najeriya wato SMEDAN Dakta Dikko Umaru Raɗɗa yace “Ba siyasa bace ta sanya muke wannan aiki, muna yi ne domin, Allah don neman lada a wajensa, kuma wannan tallafin azumin shine karo na bakwai, abinda yasa muke daukar hotuna muna nunawa duniya, don ya zama abin koyi ga wasu, su gani suma su kwaikwayi Aikin Alkhairi.” Inji Raɗɗa. Ya kara da cewa, “Idan Siyasa muke ‘yan siyasa zamu gayyato, amma sai muka gayyaci Malamai domin suyi tsokaci, kuma su kwadaitar akan muhimmancin ciyarwa, musamman a cikin azumi.” Radda ya kawo misalin ayar ciyarwa da irin ladar da ake samu ga wanda ya ciyar, inda aka karshe ya roki Al’umar da suka taru don amsar tallafin, da suyi masa Addu’a idan abinda yake nema na jagorancin jihar Katsina Alkhairi ne ga Addini da rayuwar Al’umma, Allah ya tabbatar da shi, idan kuma ba shi bane, Allah ya musanya Alkhairi.
Shima shugaban cibiyar Kabir Usman Amoga yayi jawabi na dalili da asalin kafa cibiyar, da kuma irin gudummawar da cibiyar ta bawa al’umma tsawon shekaru, bisa jajircewar Dakta Dikko Umaru Radda Gwagwaren Katsina, inda kuma yace duk wanda zai iya sadaukar da Dukiyarsa sa domin Al’umma inaga ya samu damar zama Gwamna…? Inji Amoga. A karshe yayi fatan Nasara ga Dikko Umaru Radda akan zabarsa a matsayin Gwamnan jihar Katsina domin Ayyukan Alkhairi su lillinka wanda yake.
Malama Tamadina Masanawa, Sheikh Abu Ammar, Sheikh Aminu Yammawa Dukkansu sunyi tunasarwa akan aikin Allah yin abu don Allah, muhimmancin ciyarwa jan hankali akan yin amfani da abinda aka bayar a hanyar da ta dace.