ƘADDAMAR DA TSANGAYAR ZAMANI TA ALMAJIRAI A KADUNA

#GaskiyarLamarinNijeriya @Do You know NG

Ko kun san cewa, a ranar Laraba, 10 ga Nuwamba, 2021, Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ƙaddamar da tsangayar koyar da ilimin Alƙur’ani da sauran darussan Arabiya da Musulunci a Kaduna?

Hukumar Kula da Ilimin Arabiyya da Nazarin Islamiyya a Nijeriya (NBAIS) ce ta ƙaddamar da tsangayar a ƙarƙashin kulawar Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, domin horar da malamai dabarun yadda za su ilimintar da almajiransu a zamanance.

Wannan na daga cikin ƙudirorin da gwamnatin Shugaba Buhari ta sanya a gaba, don bunƙasa zuwan yara makaranta da rage gararambarsu a gari tare da hana yin barace-barace a titinan ƙasar!

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here