Home HomeNan da kwanaki 11 zamu kulle iyakokin da suka hada Arewa da kudu__inji kungiyar IPOB.

 

Kungiyar IPOB dake Najeriya ta fitar da sanarwar cewa nan da kwanaki 11 zasu kulle duk wasu iyakoki da suka hada Arewa da kudu matukar Gwamnatin Najeriya bata sakko musu Jagoran su Nmadi KANU ba.

Kungiyar IPOB ta fitar da wannan sanarwar ne a Gidan Radion Biafra a safiyar yau Alhamis, inda take Jan kunnen Gwamnatin Najeriya data gaggauta bin wannan umarnin Na sakar musu Jagoran su kafin cikar wa’adin kwana 11, Wanda rsshin yin hakan zai haifar da kulle duk iyakokin da suka hada Arewa cin kasar da kudancin kasar.

Daga Kabiru Ado Muhd